Ebola: Ministocin Lafiya na Yammacin Afrika suna taro a Ghana
Ministocin lafiya daga kasashen yammancin Afrika suna gudanar da taro a kasar Ghana domin tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar Ebola da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo.
Wallafawa ranar:
Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da aka ci gaba da samun sabbin mutane da ke kamuwa da cutar da kuma yadda cutar ke jefa rayuwar ma’aikatan lafiya cikin hadari
Abdousalam Nasidi wanda ya wakilci Ministan Lafiya a Najeriya ya shaida RFI Hausa cewa zasu tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar a yankin Afrika ta yamma saboda yadda cutar yaduwar a cikin hanzari.
Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta yi alkawalin zata taimaka a shawo kan cutar.
Hukumar Lafiya ta duniya WHO tace kimanin mutane 467 suka mutu, tare da yin gargadin adadin na iya karuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu