Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Jonathan zai ciwo bashi

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nemi Majalisar Tarayya ta amince da bukatar ya ciwo bashin kudi dala biliyan guda daga kasashen waje domin yaki da Mayakan Boko Haram da ke addabar kasar.

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A cikin wata wasika da Shugaban ya aikawa Majalisa, Jonathan yace ya zama wajibi ya ciwo bashin kudin da suka kai Biliyan 162 na Naira don inganta tsaro musamman horar da sojoji da samar da kayan aiki.

Babu dai wani cikakken bayani a game da inda Jonathan zai ciwo bashin kudin.

A watan Fabrairu, Gwamman Borno Kashin Shettima yace Mayakan Boko Haram sun mallaki makamai fiye da Sojojin Najeriya, kalaman da Sojin suka karyata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.