Isa ga babban shafi
Ebola

WHO ta kaddamar da dokar ta baci akan Ebola

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta kaddamar da dokar ta baci akan cutar Ebola da ke kisan Jama’a a yammacin Afrika tare da neman tallafi daga kasashen duniya domin magance bazuwar cutar musamman a kasashen da Ebola ta zama annoba.

Margaret Chan, Babban Jami'ar Hukumar WHO da ke aikin cutar Ebola a Afrika
Margaret Chan, Babban Jami'ar Hukumar WHO da ke aikin cutar Ebola a Afrika REUTERS/Pierre Albouy
Talla

Wannan matakin na WHO na zuwa ne bayan Jami’an hukumar sun kammala wani taron gaggawa a Geneva game da Ebola. Hakan kuma na nufin Hukumar zata haramta wa mutane shiga wasu kasashe a yammacin Afrika akan matakan dakile yaduwar cutar da ta hallaka mutane kusan 1,000 a kasashe Uku.

Tuni Kungiyar Likitoci ta Doctors Without Borders ta bayyana cewa cutar Ebola ta zama annoba a yammacin Afrika kuma tana iya bazuwa zuwa wasu kasashe.

Cutar Ebola ta kashe mutane da dama a Guinea da Liberia da Saliyo, yayin da kuma ta kashe mutane biyu a Najeriya. Tuni wadannan kasashen suka kafa dokar ta baci domin yaki da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.