Isa ga babban shafi
Liberia

An kai hari a asibitin Ebola a Liberia

Rahotanni daga Liberia sun ce wasu gugun mutane dauke da muggan makamai sun kai hari a asibitin da ake kula da mutanen da ke dauke da cutar Ebola, kuma an ruwaito cewa 29 daga cikinsu sun tsere daga asibitin da ake kula da lafiyarsu.

Allon gargadi game da cutar Ebola a birnin Abidjan kasar Côte d'Ivoire
Allon gargadi game da cutar Ebola a birnin Abidjan kasar Côte d'Ivoire REUTERS/Luc Gnago
Talla

Jami’an lafiya da shedun gani da ido da suka tabbatar da harin sun ce ‘Yan bindigar sun kai farmakin ne dauke da kulake a asibitin ta majinyatan Ebola. Kuma sun ce dukkanin majinyatan sun tsere.

‘Yan bindigar an ji suna cewa “Karya ne babu Ebola a Liberia”, tare da ambatar shugabar Kasar Ellen Johnson Sirleaf akan ta tsiyace shi ya sa ake karyar Ebola a kasar, kamar yadda wata shedu ta tabbatar.

Kuma shedun tace Jami’an lafiya a asibitin sun tsere bayan kai harin.

Cutar Ebola dai ta yi sanadin mutuwar mutane 1,145 a kasashen Guinea inda cutar ta fara bulla da Liberia da Saliyo da kuma Najeriya da aka samu mutuwar mutane hudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.