Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ne zai fayyace makomar mataimakinsa Namadi Sambo

Jam’iyyar PDP a Najeriya ta ce shugaban kasar Goodluck Jonathan ne kawai zai bayyana wanda zai zama mataikinsa a zaben shekara mai zuwa.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo
Talla

Sakataren yada labaran Jam’iyyar Oliseh Metuh ya ce amincewa da takarar shugaba Jonathan da Jam’iyyar ta yi a matakin taron Gwamnoni da Majalisar Zartarwa cikin makon jiya babu mataimakinsa Namadi Sambo a ciki.

Metuh ya ce shugaba Jonathan zai bayyana abokin takararsa ne lokacin da zai amince da bukatar tsayawa takara a zaben da za a gudanar da a shekara mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.