Isa ga babban shafi
SYRIA

Amurka ta soma jefa wa Kurdawan Kobane makamai

Amurka ta soma jefa wa Kurdawa da manyan makamai domin yin amfani da su wajen kare kansu daga hare-haren mayakan jihadi na kungiyar IS da suka share tsawon wata daya suna yi wa birnin Kobane kawanya.

Kurdawa a kusa da iyakar Syria da Turkiyya
Kurdawa a kusa da iyakar Syria da Turkiyya Reuters/路透社
Talla

Hukumomin kasar ta Amurka sun bayyana matakin jefa wa Kurdawan makamai da cewa ya zama dole, lura da yadda mayakan na IS ke ci gaba da nuna turjiya duk da farmakin da sojojin kawance ke kai masu ta sama, yayin da suke ci gaba da fafatawa da mayakan kare kai na Kurdawa a wannan gari da ke gab da iyakar Syria da Turkiyya.

A daya bangare kuwa yanzu haka ana ci gaba da gwabza fada tsakanin mayakan na IS da kuma Kurdawan Kobane da ke samun goyon bayan kasashen duniya, fadan da kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 800.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.