Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Burkina: Amurka ta bukaci Sojoji su mika mulki ga farar hula

Gwamnatin kasar Amurka ta yi kira ga Sojojin kasar Burkina Faso su gaggauta mika mulki ga farar hula bayan mutanen kasar sun tursasawa Blaise Compaore yin murabus daga mukaminsa na shugaban Kasa wanda ya kawo karshen shugabancinsa na shekaru 27 a kasar.

'Yan adawa sun kaddamar da sabuwar zanga-zanga bayan Sojoji sun kwace mulki a Burkina Faso
'Yan adawa sun kaddamar da sabuwar zanga-zanga bayan Sojoji sun kwace mulki a Burkina Faso REUTERS/Joe Penney
Talla

Amurka ta yi Allah wadai da kwace mulki da Sojojin kasar suka yi, tare da gargadin kakabawa kasar takunkumi.

A jiya Assabar ne Sojojin kasar suka amince da zaben Kanal Isaac Zida a matsayin sabon shugaban kasa wanda zai jagoranci kasar har zuwa lokacin da aka gudanar da sabon zabe.

Mutanen Burkina Faso dai sun tursasawa Compaore yin murabus bayan sun kwashe kwanaki hudu suna zanga-zangar adawa da shirinsa na sauya kundin tsarin mulki domin ba shi damar yin tazarce.

Amurka tace ya dace ace Sojojin kasar sun mutunta kundin tsarin mulkin kasar. domin a tsarin dokar Burkina Faso, Kakakin Majalisa ne ya kamata ya zama shugaban rikon kwarya, kafin Sojoji su kwace mulki.

Kanal Zida ya yi alkawalin zai jagoranci gudanar da sahihin zabe a kasar domin dawo da Burkina Faso a turbar mulkin dimukuradiya.

Sai dai kuma ‘Yan adawa da kungiyoyin fararen hula sun yi kira ga al’ummar kasar su fito domin kaddamar da sabuwar zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.