Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan bindiga sun kai hari a Nafada

‘Yan bindga da ake tunanin mayakan Boko Haram ne sun kaddamar da hare hare a garin Nafada na jihar Gombe a arewacin Najeriya, inda suka kona Ofishin ‘Yan sanda da na Jam’iyyun siyasa. Wani shedun gani da ido yace ‘Yan bindigar sun shigo garin ne acikin motoci da babura, amma yace babu wanda suka kashe.

Aboubakar Shekau Shugaban Mayakan Boko Haram a Najeriya
Aboubakar Shekau Shugaban Mayakan Boko Haram a Najeriya AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Garin Nafada yana kan iyaka ne da Jihar Yobe, da ke fama da hare haren Boko Haram. Shedun yace 'Yan bindigar sun shiga banki suka kwashi kudi.

Rahotanni sun ce Mayakan na Boko Haram sun kori Jami'an tsaro a garin, tare da kafa tutarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.