Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An sake kai wa wani dan wasa hari a Afrika ta kudu

‘Yan bindiga sun sake kai hari a gidan iyayen wani dan wasan Afrika ta kudu Sibusiso Vilakazi hari, a lokacin da ya ke bacci a gidan iyayen a Johannesburg. ‘Yan sanda sun tabbatar da kai harin a garin Soweto.

Senzo Meyiwa Jagoran 'Yan wasan Afrika ta kudu da aka kashe.
Senzo Meyiwa Jagoran 'Yan wasan Afrika ta kudu da aka kashe. REUTERS/Siphiwe Sibeko/Files
Talla

‘Yan bindigar sun shiga gidan iyayensa ba tare da sanin dan wasan ba saboda yana bacci a bayan gidan har sai da suka fita.

Sai dai babu wanda ‘yan bindigar suka kashe, Amma ‘yan bindigar sun ambaci sunansa tare da karbar makullin motarsa da wayoyin salula na iyayen da kudi da zinari.

Dan wasan yace ‘Yan bindigar sun shiga ne domin halaka shi.

‘Yan bindigar sun kai wa dan wasan hari ne a ranar Assabar, duka mako guda bayan kisan Jagoran ‘Yan wasan Afrika ta kudu Senzo Meyiwa, wanda aka bindige a gidan budurwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.