Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Jonathan dan takarar PDP

Yau Talata ne, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ke kaddamar da takarar sa na zaben shekara mai zuwa a karkashin Jam'iyar PDP. Bukin na yau za'a gudanar da shi ne a birnin Abuja inda magoya bayan sa daga kowane sako na kasar zasu halarta tare da manyan ya’an jam'iyar PDP

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Talla

Gwamnonin jihohi, ministoci da kuma shugabanin hukumomin gwamnati daga sassa daban daban na kasar ne za su isa Abuja domin nuna goyan bayan su.
Farfesa Rufai Ahmed alkali mai baiwa shugaba Jonathan shawara kan harkokin siyasa yace kungiyoyi sama da 8,000 suka nemi shugaban ya sake tsayawa takara saboda gamsuwa da yadda yake tafiyar da mulkin sa a cikin gaskiya da adalci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.