Isa ga babban shafi
Senegal

Hollande ya ce faduwar gwamnatin Blaise Campaore Darasi ne ga shugabannin Afruka

Gabanin taron kasashen “Francophonie” shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana zanga-zangar data yi sanadin saukar shugaban kasar Burkina Faso a matsayin Darasi ga sauran shugabannin Afruka

Le président François Hollande lors de l'interview avec RFI, France 24 et TV5 Monde.
Le président François Hollande lors de l'interview avec RFI, France 24 et TV5 Monde. FMM
Talla

Har ila yau shugaban ya tabo wasu batutuwa da suka shafi kasar Faransa da kuma sauran kasashen Duniya kamar batun yaki da ta’addaci, da taron kasashe renon Faransa a Senegal da rikicin kasar Libya da na Isra’ila da Falasdinu.

A ranar assabar 29 zuwa 30 ga wannan wata na Nuwamba ne, za a soma zaman taron shugabannin gwamnatocin kasashen kungiyar kasashe masu amfani da Harshen Faransanci wato “Francophonie” na Duniya karo na 15 a kasar Senega.

zaman taron da zai maida hankali ne kan wanda zai gaji tsohon shugaban kasar Senegal Abdu Diouf daga kan kujerar shugabancin kungiyar bayan ya shere tsawon shekaru 12 yana shugabancinta.

Kawo yanzu dai babu wani daga cikin ‘yan takara 5 da shuwagabannin kasashen suka cimma jituwa a kansa, haka kuma a hukumance kasar Fransa ba ta da dan takara, to amma duk da haka kasar nada abin cewa akan haka, bisa la’akari da karfin fada ajin da take da shi a cikin kungiyar.

Ginshikin ita wannan kungiya ta Francophonie dai, shi ne yada yaren na faransanci, inda kasar Faransa ke da muhimmin matsayin na tsakkiya a kungiyar.

A yau kamar yadda Alkalumma kungiyar ta OIF suka nunar, mutane miliyan 274 ne ke magana da amfani da yaren na faransanci a hukumance a Duniya baki daya.

A yayinda kashi 55% na mutanen ke a Nahiyar Afrika, kashi 37% kuma na a Nahiyar Turai.

Kungiyar ta OIF ta bayyana fatan ganin cewa, nan da shekarar 2050, yawan mutanen da ke magana da yaren na faransanci a Duniya za su kai 770.

Manufar kungiyar kuma ita ce, kokarin sake mayar da yaren na faransanci a matsayin babban yaren da za a dinga zartar da daukar wasu manyan matakai na Duniya da shi, musaman wajen bunkasa harakokin saye da sayarwa tsakanin al’ummomin Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.