Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kai hari a Bajoga da Ashaka

‘Yan bindiga da ake zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari a garin Bajoga da ke Jihar Gomben Najeriya, wani mazauni garin ya shaidawa RFI Hausa cewa da sanyin safiyar Alhamis ne ‘Yan bindigar suka abkawa garin.

Hare haren Boko Haram a garin Damaturu jihar Yobe
Hare haren Boko Haram a garin Damaturu jihar Yobe Reuters/Olatunji Omirin
Talla

Bayanai sun ce Maharan sun shigo ne daga arewacin garin Bajoga suna ta harbe harbe harben bindigogi ba kyafkyaftawa.

Shedun yace Maharan sun kori ‘yan sanda a garin, lamarin da ya ba mutanen garin tsoro suka gujewa gidajensu.

00:32

Mazauni garin Bajoga

Rahotanni sun ce Maharan sun karbe wani yanki na Bajoga tare da shiga Ashaka.

Zuwa yanzu babu wani bayani daga Jami’an tsaro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.