Isa ga babban shafi
DRC Congo

Za’a rage Dakarun Majalisar dunkin Duniya a JD Congo

Majalisar dunkin Duniya ta ce mai yuwa ne ta rage yawan Dakarunta masu aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo wanda shi ne mafi girman aikin da take a dukkanin fadin Duniya

forte.jor.br
Talla

Majalisar dai ta ce mai yuwa ne wannan shirin rage Dakarunta ya fara aiki daga shekara mai kamawa ta 2015, idan dai aka maido da Doka da Oda a cikin kasar.

Haka kuma Majalisar ta Dunkin Duniya ta bayyana damuwa da yadda al’amurra ke dada tsauri a yankin Arewacin Lardin Kivu, inda ake da Dakarun kasar Congo da na kasashen ketare da dama.

Martin Kobler jagoran Dakarun kwantar da tarzoma na MONUSCO a kasar ta Congo, ya ce hakan na iya kasancewa, kama daga shekarar 2015 idan an kai ga kafa Gwamnati a kasar ta Congo.

Kobler yace tuni da aka tura Tawagar kwararru daga Ofishin Majalisar dunkin Duniya na birnin new York a kasar Amurka a Congo, domin duba yanda shirin rage Dakarun zai soma aiki.

Yanzu haka dai yankin Bani na Arewacin kasar na zaman mafi hatsari inda a baya aka kashe akalla mutane 200 dag aWatan Okotoba zuwa Nuwamba.

Daga cikin wadanda aka fi kashewa kuwa hadda Mata da kananan yara da ko ma aka kashe ta hanyar suka da Wuka, ko kuma makurewa da gangan har su mutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.