Isa ga babban shafi
Algeria-Niger

Algeria ta fara korar ‘Yan Nijar

Kasar Algeria ta fara aikin taso keyar dubban mutanen Nijar da suka shiga kasar ta barauniyar hanya, inda tuni Firaministan Nijar Birgi Rafini ya bukaci mahukuntan kasar su koro ‘Yan Nijar da ke zaman bansa da yawon bara a Algeria.

Yankin Tamanrasset da mutanen Nijar ke shiga  kasar Algeria
Yankin Tamanrasset da mutanen Nijar ke shiga kasar Algeria AFP/Fayez Nureldine
Talla

Algeria za ta fara taso keyar ‘yan Nijar 318 zuwa Agadez, wadanda yawancinsu Mata ne da kananan yara.

Tun dai lokacin da kasar Libya ta shiga rikici, mutanen yankin Kudancin Sahara suka mayar da zango a Algeria domin samun rayuwa mai inganci.

Algeria tace za a dauki lokaci kafin kammala aikin kwashe ‘Yan Nijar daga kasar.

A watan Oktoba mutanen Nijar kimanin 92 suka mutu a Sahara saboda tsananin zafi da kishirwa a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa Algeria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.