Isa ga babban shafi

Faransa tace ta karya lagon ayyukan ta'addanci a Mali

Dakarun sojojin Faransa sun ce akalla sun kame mayakan jihadi kusan 200 a yankin Sahel dake yammcin afrika a cikin shekarar da ta gabata. Minister tsaron kasar Jean-Yves-Le Drian yace wannan ya karya lagon ayyukan mayakan jihadi a yankin na Sahel. A lokacin da yake zantawa da gidan Rediyon Faransa, Jean Yves Le Drian ya ce a wani jerin samame da suka kaddamar akan yan ta’ada a kasashe 5 dake yankin Sahel, sojojin kasar sun kame akalla yan ta’ada 200 cikin su har da wasu muhimman shugabanin yan ta’adan, wadanda yawanci aka cafke su a kasashen Niger da MaliA dai satin daya gabata ne dakarun Faransa suka bada sanarwa kashe wani dan asalin kasar Mali mai suna Ahmed el-Tilemsi, wanda ke shugabantar kungoyoyin jihadi a Algeria.A shekarar ta 2013 ne dakarun suka yi nasarar cafke da dama daga cikin mayakan jihadin, wadanda ke iko da wasu yankuna kasar Mali. A watan Augustan wannan shekara kuma suka kara kaddamar da wani samame don cigaba da kame da nufin kawo karshen masu rikici jihadi a yankuna kasashen Afrika.Yanzu haka akwai akalla dakarun Faransa dubu 3 dake aiki a Mali, Mauritania, Niger, Burkina Faso da kuma chadi Le Drian ya bukaci kasashe su dau matakai wajen bada gudumawa a kasashe dake fama da ta’adanci.  

Sojojin Faransa a kan hanyar su ta zuwa Mali daga Chadi
Sojojin Faransa a kan hanyar su ta zuwa Mali daga Chadi REUTERS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.