Isa ga babban shafi
Nigeria

Jam'iyyar APC na gab da bayyana wanda zai mata takarar maimakin shugaban Nigeria

Tun bayan kammala zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC mai adawa a Nigeria, ‘yan kasar ke ta rade radin wanda jam’iyyar zata tsayar dan takarar mataimakin shugaban kasa, da zai yi aiki tare da Janar muhammadu Buhari, da aka zaba a makon da ya gabata, a matsayin dan takarar shugabancin kasar. Mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC mai kula da yankin arewacin kasar, Sanata Lawal Shu’aibu, yace yau litinin shugabanin jam’iyyar zasu yi taro a Abuja, don yanke shawara kan wanda za a tsayar.Sanata Shu’aibu yace an baiwa shugabannin jam’iyyar da suka fito daga kudancin Nigeria damar fidda dan takarar mataimakin shugaban kasa.Sai dai jam’iyyar PDP mai mulki ta bayyana cewa, Janar Buhari yayi watsi da ‘yancinsa na zaben mataimaki, don haka a cewar jam’iyyar, Janar din ya fiye sanyi. 

Dan takarar shugabancin Nigeria karkashin jam'iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari
Dan takarar shugabancin Nigeria karkashin jam'iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.