Burkina Faso
An dakatar da Jam’iyyar Campaore a Burkina
Gwamnatin Rikon kwaryar kasar Burkina Faso ta sanar da dakatar da Jam’iyyar tsohon shugaban kasar Blaise Campaore da ke gudun hijira a Cote d’Ivoire saboda karya dokar kasa. Ministan cikin gida Auguste Denise Barry yace bincike ya nuna Jam’iyar na daukar matakan da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasar dalilin da ya sa suka dauki mataki akan dakatar da ayyukanta.
Wallafawa ranar:
Talla
A ranar 31 ga watan Oktoba ne Compaore ya fice Burkina Faso bayan kawo karshen mulkinsa na shekaru 27.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu