Isa ga babban shafi
Masar

Kotun Masar ta haramta bikin Yahudawa

Wata Kotun kasar Masar ta haramtawa Yahudawa gudanar da bikin da suke yi duk shekara domin karrama ranar haihuwar mashahurin Malaminsu na Morocco Yakuba Abu Hasira. Kotun tace bikin ya sabawa al’adun Misra.

Yahudawa na karrama kabarin Abu Hasira a kasar Masar
Yahudawa na karrama kabarin Abu Hasira a kasar Masar alarabiya.net
Talla

Ana gudanar da bikin ne a Nile Delta a lardin Baheira.

Kotun birnin Alexandria ne ta haramta gudanar da bikin wanda Yahudawa ke gudanarwa a watan Janairu tun shekarar 1979, a lokacin da Masar da Isra’ila suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Yahudawa da dama daga kasashen Isra’ila da Faransa da Amurka da Morocco ke kawo ziyara Masar domin karrama Kabarin Abu Hasira a kauyen Dutmo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.