Isa ga babban shafi
Nijar

Za a soma Shari’ar Hama Amadou

Rahotanni daga Jamhuriyyar Nijar na cewa a ranar Juma’a ne za a fara shari’ar tsohon shugaban Majalisa Hama Amadou ba a gaban idonsa ba idan har bai dawo ba kafin soma Shari’ar kan zargin da ake masa na mallakar ‘ya’yan da aka yi fataucinsu daga Najeriya.

Tsohon Shugaban Majalisar Nijar Hama Amadou
Tsohon Shugaban Majalisar Nijar Hama Amadou AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Hama Amadou babban mai adawa da shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya gudu zuwa Faransa, kuma za a fara shari’ar zargin da ake masa ba a gaban idon shi ba tare da wasu mutane 20 ciki har da matarsa da aka bayar da belinsu kan badakalar mallakar ‘ya’ya ba bisa kan ka’ida ba.

Wannan dai babbar barazana ce ga Hama Amadou da magoya bayan shi da ke shirin tsayar da shi takarar shugaban kasa a zaben 2016.

Laifin mallakar ‘ya’ya ga matar da ba ta haihuwa ya shafi hukuncin dauri daga shekaru biyu zuwa Takwas a gidan yari.

Batun cinikin ‘ya’ya ya soma ne tun a watan Yuni amma wasu na danganta al’amarin da siyasa.

A cikin watan Nuwamba ne Hukumomin kasar Nijar suka yi wa mutane 16 sakin talala daga cikin wadanda ake zarginsu da cinikin jirajirai.

Ministan ayyukan Noma Abdou Labou da matarsa suna cikin wadanda aka saki.

Hama Amadou babban mai adawa da shugaba Issoufou ya fice Nijar ne a watan Agusta bayan majalisa ta amince a kaddamar da bincike akansa game da badakalar mallakar ‘ya'ya ba bisa ka’ida ba da aka yi wa Matarsa fataucinsu daga Najeriya zuwa Cotonou.

Hama Amadou ya ce zargin da a ke ma sa yarfe ne na siyasa, kuma ya ce zai iya kare kansa a gaban mahukuntan Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.