Isa ga babban shafi
Libya

Tattaunawar sulhu a Libya na samun ci gaba

Yau juma’a an shiga rana ta uku a ci gaba da tattaunawar sulhu domin samar da zaman lafiya tsakanin bangarori masu rikici da juna a kasar Libya, tattaunawar da ke gudanar a birnin Geneva karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Taron Geneva kan Libya
Taron Geneva kan Libya AFP
Talla

A tsawon kwanaki biyu da suka gabata, tattaunawar ta yi matukar armashi sakamakon yadda wakilai daga bangarorin da ke hamayya da juna suka bayyana fatar an samu zaman lafiya, Kamar dai yadda ofishin MDD a kasar Libya ya bayyana a wata sanarwar.

Manzon musamman na MDD a kasar Bernardino Leon, da farko ya bayyana fargabarsa a game da yiyuwar samun ci gaba a lokacin wannan ganawa ta birnin Geneva, to sai dai lura da yadda ake gudanar da tattaunawar a cikin fahinta, wannan ya karfafawa masu shirya taron gwiwa game da yiyuwar samar da mafita ga rikicin da kasar ta Libya ke fama da shi kusan shekaru 4 da suka gabata.

Babbar manufar taron dai ita ce cimma matsaya domin kafa gwamnatin hada-ka tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna a kasar wanda hakan zai kawo karshen hauloli masu bambanci ra’ayi ke iko da yankuna a maimakon gwamnatin tsakiya.
Yanzu haka dai gwamnatin kasar wadda kasashen duniya suka amince da ita, na zaune ne a garin Tobruk da ke gabashin kasar bayan da ‘yan tawaye suka kore ta daga Tripoli.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.