‘Yan Sanda sun bude wa masu zanga-zanga wuta a Congo
Rahotanni daga Jamhuriyar Congo na cewa ‘Yan sanda sun yi harbin bindiga a arangamar da suke yi da daliban Jami’a da ke zanga-zanga a birnin Kinshasa a yau Laraba. Akalla mutane 28 suka mutu tun fara kaddamar da zangar-zangar ta adawa da shirin gwamnati na sauya kundin tsarin mulki.
Wallafawa ranar:
Wakilin Kamfanin Dillacin labaran Faransa ya ruwaito cewa ‘Yan sanda sun bude wa masu zanga-zanga wuta.
Sai dai Hukumomin kasar sun ce mutane biyar ne suka mutu a zanga-zangar ciki har da Dan Sanda guda da wasu daliban Jami’ar Kinshasa biyu lokacin da bangarorin biyu suka yi arangama.
A ranar Litinin ne mutanen Congo suka kaddamar da zanga-zangar adawa da shirin gwamnati na sauya kundin tsarin mulki domin ba Joseph Kabila damar ci gaba da shugabanci a kasar.
Matasa sun yi kone wasu gine ginen gwamnati a Kinshasa, yayin da fursunoni da dama suka tsere a gidan yari.
‘Yan adawa yanzu sun kira wani gagarumin gangami domin neman shugaba Kabila ya yi murabus wanda ya kwashe shekaru 14 yana shugabanci a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu