Isa ga babban shafi
Boko Haram

Majalisar Nijar za ta kada kuri’ar amincewa a tura dakaru Najeriya

Majalisar kasar Nijar za ta kada kuri’ar amincewa da matakin aikawa da dakaru domin yakar Mayakan Boko Haram na Najeriya a ranar Litinin. Ana sa ran Majalisar za ta amince da bukatar tura dakarun kamar yadda shugaban kasa Mahammadou Issoufou ke bukata.

Sojojin Nijar a kusa da yankunan da Boko haram ta kwace a kan iyaka da Najeriya
Sojojin Nijar a kusa da yankunan da Boko haram ta kwace a kan iyaka da Najeriya RFI/ Nicolas Champeaux
Talla

Wata majiyar gwamnati tace Majalisar za ta yi zama a ranar Litinin domin amincewa da bukatar Shugaba Mahammadou na aikawa da dakaru don yakar Boko Haram na Najeriya.

Dakarun Nijar za su hada kai ne tare da dakarun Chadi da Kamaru da Najeriya domin yakar Boko Haram da ke barazana ga kasashen.

Rahotanni sun ce tuni dakarun Chadi suka kafa sansani a yankin Bosso na Nijar da ke kan iyaka da Najeriya.

Ana sa ran ‘yan adawa a Nijar za su amince da bukatar Shugaba Issoufou na shiga yaki da Boko Haram.

Bako Haram dai ta karbe garuruwa da dama a yankin arewa maso gabacin Najeriya ciki har da garin Baga da ke kusa da tabkin Chadi, magamar Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya.

Ana sa ran dakarun Nijar za su yi kokarin karbe ikon garuruwan da ke kan iyaka da ita na Najeriya, Malam Fatori da Damasak da ke hannun ikon Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.