Bakonmu a Yau
Sojojin Chadi sun ja daga a Nijar da nufin tsallakawa Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:13
Yanzu haka dubban sojojin kasar Chadi na can sun ja daga a garuruwa da dama na jihar Diffa da ke jamhuriyar Nijar, a yunkurinsu na kutsawa domin fatattakar ‘yan Boko Haram a Tarayyar Najeriya.Malam Madu, wani mazauni garin Bosso ne inda aka jibge wani adadi na sojojin kasar ta Chadi, ya yi Abdoulkarim Ibrahim Shikal karin bayani a game da abinda ke faruwa a yanzu haka.