Isa ga babban shafi
Somalia

An kashe Kwamandan Al Shebaab na Somalia

Kuramen Jiragen yakin Amurka sun kashe wani babban kwamandan Mayakan Al shebaab na Somalia a hare haren da suka kaddamar a kudancin birnin Mogadishu. Gwamnatin Somalia ta tabbatar da mutuwar kwamandan mai suna Yusuf Dheeq wanda aka kashe a ranar Assabar din da ta gabata.

Mayakan Shabab na Somaliya
Mayakan Shabab na Somaliya REUTERS / Feisal Omar
Talla

Dheeq shi ke jagorantar ayyukan leken asirin Al Shebaab tare da shirya tsarin tsaron kungiyar.

Gwamnatin Somalia tace kisan kwamandan nasara ce ta tabbatar da zaman lafiya a kasar.

A cikin wata sanarwa, Gwamnatin Somalia ta bukaci mayakan al Shabaab su mika kai tare da ajiye makamansu saboda yadda ake kisan shugabanninsu.

Amma masana na ganin kisan shugabannin ba zai kawo karshen ayyukan al Shebaab ba lura da yadda ta faru da Boko Haram na Najeriya da suka kaddamar da hare hare bayan kashe Shugabansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.