Isa ga babban shafi
Nigeria

Daga jaridun Nigeria

Bayan a jiya Asabar aka gudanar da zaben shugaban kasa a Nigeria, yau lahadi jaridun kasar da dama sun dauko labarun da wasu jaridar kasar suka mayar da hankali, inda akasarin jaridun suka duba yadda zaben na jiya Asabar ya gudana, Nasiruddeen Muhammad ya duba wasu daga jaridun, ga kuma abinda ya kalato.Jaridar THE PUNCH da ake bugawa a Kudancin Nigeria ta rawaito cewa Tshohon Shugaban Nigeria, kuma dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar adawa ta APC ya kayar da Shugaba Goodluck Jonathan a akwatin dake cikin fadar shugaban, yayin zaben da aka yi a jiya Asabar.Jaridar THE NATION da ake bugawa a birnin Lagos ta dauko labarin dake cewa wasu daga cikin manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da suka hada da Olabode Geoge, Musliu Obanikoro, Femi Fani Kayode da dan takarar gwamnan jihar Lagos, karkashin jam’iyyar PDP Jimi Agbaje, duk sun sha kaye a mazabunsu.Jaridar ta kara da cewa mazabun tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Bola Tinubu da kuma Janar Muhammadu Buhari, duk APC ce ta lashe.Jaridar LEADERSHIP da ake bugawa a Abuja ta dauko labarin da ke cewa jam’iyyar PDP mai mulki tayi rawar gani a jihar Bayelsa, mahaifar shugaba mai ci Goodluck Jonathan.Jaridar PEOPLE DAILY da ake bugawa a birnin Abuja tace dan takarar shugabancin kasar karkashin jami’iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben da aka yi a jihohin dake hannun jami’iyyar tashi.Jaridar ta bayyana jihohi kamar su Kano, Lagos da Sokoto da sauransu, a matsayin wasu daga cikin jihohin da ‘yan adawan suka yiwa PDP fintinkau.Jaridar VANGUARD kuma, ta nuna yadda jama’a suka kai dare suna kada kuri’a a sassan kasar, bayan da aka warware matsalar da aka samu da na’urorin tantance masu zabe a wasu wuraren. 

Wasu jama'a suna duba Jaridun Nigeria
Wasu jama'a suna duba Jaridun Nigeria © AFP/Pius Utomi Ekpei
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.