Isa ga babban shafi
morocco

'Yan asalin Spain da ke binciken tarihi sun bace a Morocco

Wasu mutane uku ‘yan Kasar Spain sun bace a lokacin da suke kokarin gano wuraren tarihi a kasar Morocco  

Reuters
Talla

Mutanen na cikin tawagar mutane 9 dukkanin su ‘yan asalin kasar Spain da suka ziyarci kasar Morocco da zummar bincike domin gano wuraren tarihi a wani yanki da ke da tarin manyan tsaunuka, yayin da suka raba kansu domin aiki a bangarori dabam dabam.

‘Yan uwan mutanen dai, sun daga hankulansu ne bayan shafe kwanaki biyu ba tare da ganin mutanen ba, lamarin da ya sa suka sanar da hukumomin yankin halin da suke ciki.

Tuni dai hukumomin yankin suka bada umarnin nemo mutanen, inda suka tanadi jirage masu saukan angulu da motoci domin shige da fice a tsakan kanin yankin da zummar gano inda mutanen suka makale.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.