Isa ga babban shafi
Nigeria

Shugaba Jonathan Na Nigeria Ya Gana Da Janar Buhari

A Nigeria Shugaban kasar mai barin Gado Goodluck Jonathan da Shugaba mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari sun kwashe wani lokaci mai tsawo suna tattaunawa gaba da gaba tare a fadar Aso Rock.Majiyoyi na cewa wannan shine karo na farko kuma baya rasa nasaba da shirin mika mulki kamar yadda wasu kafofin labarai suka yi ta yada wani sauti na Shugaba Goodluck Jonathan na gayyatar Janar Buhari.Ranar Asabar mai zuwa ne dai , mutan Nigeria za su sake zuwa tashoshin jefa kuri'u domin zaben Gwamnoni da wakilan majalisar Dokoki a jihohi.Wasu bayanan da muke samu daga jihohin kasar na cewa  kamar jihar Lagos na cewa 'yan takaran jamiyu 10 sun dunkule domin neman magoya bayansu sun zabi dan takara daya. 

Shugaba Goodluck Jonathan tare da Shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari
Shugaba Goodluck Jonathan tare da Shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.