An kaddamar da harin sama a Sansani Al-Shabab
Jiragen yaki a Kenya sun yi luguden wuta a kan sansanonin mayakan al-Shabab da ke makwabciyar kasar a Somalia.Wannan dai shine karon farko da dakarun Kenya ke kai wa 'yan Kungiyar al shabaab hari tun bayan harin da aka Jami'ar Garissa a cikin makon jiya, wanda da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 148.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun Dakarun sojin kasar David Obonyo ya sanar da cewar, sun kona sassani mayakan biyu a harin da ake kai musu ta jiragen saman yaki kenya
lamarin dai na zuwa ne a wannan lokaci da ka shiga ranar ta biyu na zaman makoki harin Jami’ar Garissa
Shugaban kasar Kenya Uhurru Kenyatta yayi alkawarin daura damarar yaki da ta’adanci a kasar, bayan faruwar harin Garissa, da ya matukar haddasa tsoro a zukatan al’ummar kasar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu