Isa ga babban shafi
MDD-Najeriya

Boko Haram: MDD za ta taimakawa ‘Yan gudun hijira

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar tallafin kudi sama da dala Miliyan 174 domin taimakawa ‘Yan gudun hijirar Najeriya da suka tsere zuwa kasashen Chadi da Nijar da Kamaru saboda rikicin Boko Haram.

Sansanin 'Yan gudun Hijirar rikicin Boko Haram a Kamaru.
Sansanin 'Yan gudun Hijirar rikicin Boko Haram a Kamaru. REUTERS/Bate Felix Tabi Tabe
Talla

Shirin da aka kaddamar a Birnin Dakar da ke kasar Senegal ya samu halartar manyan baki, cikin su har da Jakadan Majalisar na musamman kan harkar noma da samar da abinci da wakilan siyasa da  kungiyoyin bayar da agajin jinkai, da kuma shahararen mawakin nan dan kasar Senegal Yousifou Ndour, inda suka tattauna halin da rikicin na Boko Haram ya jefa miliyoyin jama’a a ciki.

Sun kuma tattauna yadda rikicin na Boko Haram ya shafi sauran kasashen da ke makwabtaka da Najeriya, da suka hada da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar.

Tuni dai hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, wasu daga kasashe yankin yammacin Afrika na fuskantar barazanar rashin tsaro, da kuma matsalar rashin wadatanccen abincin da ake fuskanta a yankin Sahel, da sauran matsaloli irin na Siyasa.

Hukumar ta bayyana cewa shekarar 2015 shekara ce da ake gudanar da zabubbukan shugabancin kasa a wasu kasashe na yammacin Afrika, da suka hada da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso, da Ghana da Togo da kuma Najeriya da ta kasance zakaran gwajin dafi a zaben da aka gudanar da ya haifar da canjin gwamnati ba tare da faruwar tashin hankali da aka yi tunani faruwarsa tun da farko ba.

Akan haka Hukumar ta bayyana cewa tanadin matakan gaggawa ya dace domin tunkarar yiyuwar ambaliyar jama’a, idan har aka fuskanci rigingimu a wadannan zabubbukan.

Haka kuma ta bayyana, kafa wani kwamitin kwararru da ta dorawa nauyin zura ido tare da nazarta matsayin barazanar da ake ganin za a iya fuskanta domin sanar da ita.

 Rikicin Boko Haram da ya fara tun a cikin shekarar ta 2009, kawo yanzu ya yi ajali mutane sama da 13,000 a arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.