Isa ga babban shafi
Togo

An kaddamar da yakin neman zabe a Togo

An kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasar Togo wanda za a gudanar a ranar 25 ga watan nan na Afrilu yayin da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta bukaci ‘yan siyasa su mutunta juna tare da bin doka

Shugaba Faure Gnassingbe na Kasar Togo
Shugaba Faure Gnassingbe na Kasar Togo © Mustafa Yalcin / Anadolu Agency
Talla

Tuni dai jam’iyyun siyasar kasar suka kaddamar da yakin neman zabensu, a yayin da ya rage saura mako biyu a gudanar da zaben na shugaban kasar.

‘Yan takara 5 ne ke neman kujerar shugabancin kasar ta Togo, kuma shugaban hukumar zaben kasar mai zamanta, Taffa Tabiou ya bukaci ‘yan takara da magoya bayansu su mutunta juna tare da bin doka don kaucewa tashin hankali.

A karshen makon nan ne shugaban kasar mai neman yin tazarce Faure Gnassingbé, zai hada gangami domin kaddamar da yakin neman sake zabensa karo na uku

Akwai kuma babban mai adawa da shi Jean-Pierre Fabre, shi ma wanda tuni ya kaddamar da yakin neman zabensa.

Masu sharhi dai na ganin shugaban kasar Gnassingbe ne zai lashe zaben wanda ya dare karagar mulki bayan mutuwar mahaifinsa wanda ya shafe shekru 38 yana jagorantar kasar.

A tsarin dokar Togo mutun na iya ci gaba da mulki sabanin wasu kasashen Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.