Isa ga babban shafi
Kenya-Somalia

Dalibin jami'a ya mutu sakamakon firgici a kasar Kenya

Dalibi daya ya rasa ransa a wani turmutsutsu da ya auku a jami’ar Nairobi dake kasar Kenya. Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar transfomar wutar lantarki, inda dalibai suka zaci hari aka kaddamarwa makarantarsu.Al-amarin ya faru ne da sanyin safiyar yau lahadi, kuma kimanin dalibai 100 ne suka samu raunuku a turmutsutsun da ya faru a dakunan kwanan daliban jami’ar ta birnin Nairobi.Daliban sun razana ne da karar fashewar Transfomar ta wutanr lantarkin, inda suka zaci ko ‘yan bindiga ne suka shigo makarantar don kaddamar masu da hari, Lura da cewa kwanan nan wasu ‘yan bindiga suka kai hari a jami’ar Garissa dake Kenyan, inda suka kashe kimanin mutane 150.Shuggaban Jami’ar Peter Mbithi ya shaidawa manema labarai cewa, dalibin da ya rasa ran nasa na cikin daliban da suka duro daga hawa na biyar na benen dake dauke da dakunan kwanan daliban.Wanin shaidan gani da ido ya yi Karin bayani akan lamarin, inda yace dalibai mata ne suka fara razana inda suka kwalla ihu, daga bangaren dakunan kwanan su, lamarin da ya sa suma dalibai maza suka firgita kuma kowa yayi koarin tserewa.Kungiyar Al-shabab ce ta yi ikirarin kaddamar da harin jami’ar Garissa na ranar 2 ga wannan wata na Aprilu. 

Shugabar Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugabar Kenya, Uhuru Kenyatta Kenyagvt
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.