Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Jam'iyyar Shugaba Ouattara Ta Amince Ya Zarce

Jam'iyyar dake mulki a kasar Cote d’Ivoire ta amince wa Shugaban kasar Alassane Ouattara da ya sake tsayawa takaran shugabanci a zaben  dake tafe cikin watan 10 na wannan shekaran.A wani kasaitaccen buki da aka shirya a Abidjan wani tsohon Shugaban kasar Henri Konan Bedie ya sanar da amince wa Alassane Ouattara ya zarce da mulkin.Bukin ya sami halarcin Shugaba Ali Bongo na kasar Gabon.Mai shekaru 73 Shugaba Alassane Ouattara ya hau kujeran mulkin ne a shekara ta 2011 bayan kazamin yamutsi bayan zabe a lokacin da tsohon shugaba da ya sha kaye Laurent Gbagbo ya yi kememe yaki yarda ya mika mulki.   

Shugaba Alassane Ouattara yayin da yake marhabin da shugaban Faransa Francois Hollande a Abidjan a bara
Shugaba Alassane Ouattara yayin da yake marhabin da shugaban Faransa Francois Hollande a Abidjan a bara REUTERS/Luc Gnago
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.