Isa ga babban shafi
Kenya

Kenya tace ba zata yi wa yan gudun hijirar Somaliya korar wulakanci ba

Gwamnatin kasar Kenya ta bada tabbacin cewa, duk da cikan wa’adin da ta bayar don rufe sansanin ‘yan gudun hijiran kasar Somalia, dake Kenyan ba za a yi wa ‘yan gudun hijiran Koran wulakanci ba.

sansanin yan gudun hijirar Somaliya  na Dadaab a kasar kenya
sansanin yan gudun hijirar Somaliya na Dadaab a kasar kenya
Talla

Sakamakon kazamin harin da aka kai a jamiar Garrissa a kasar Kenya, da mayakan kungiyar Alshabab na Somalia suka dauki alhakin kaiwa,

Mataimakin Shugaban kasar ta Kenya William Ruto ya baiwa MDD wa’adin watanni uku da ta san yadda za ta yi da ‘yan gudun hijiran Somalia dubu 336 dake wannan sansani

Ali Bunow Korane Shugaban Hukumar kula da ‘yan gudun hijira na kasar ta Kenya’ ya bada tabbacin cewa idan wa’adin ya ciki ba za’a wulakanta ‘yan gudun hijiran ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.