Isa ga babban shafi
Ghana-Cote D'ivoire

Shugaba Ouattara ya gana da John Dramani na Ghana a Geneva

Wata Kotun duniya ta baiwa kasar Ghana umurnin daina hako mai a cikin tekun da suke takaddama da kasar Cote d’Ivoire har sai ta kamala shari’ar dake tsakanin kasashen biyu.A jiya litinin ne shugaban kasar Cote D’Ivoire Alassane Ouattara ya gana da Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama kan wanan takaddama,sai dai wanan haduwa bata haifar da wani sakamako na kwarai ba. 

J.A-ECO
Talla

Kasar Cote d’Ivoire ne ta ruga kotun dan ganin an bi mata kadi a takaddamar da take da Ghana dan mutunta dokar hakar mai a ruwa.
Gwamnatin kasar ta bukaci kotun dake Hamburg na kasar Jamus da ta dakatar da duk wani aikin hako man da Ghana keyi har sai an kamala shari’ar.
Kasashen biyu dai na rikici kan iyakar da ta hada su kuma nan ne aka samu mai a cikin teku, wanda tuni kasar Ghana ta fara hako shi.
Kokarin sasantawa tsakanin kasahsen ya citura abinda ya sa Cote d’Ivoire ta kai kara kotun dan warware matsalar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.