Isa ga babban shafi
Burundi

Shugabannin Afrika na taro kan rikicin Burundi

Shugabannin kasashen gabacin Afrika za su gudanar da taro a Tanzania domin tattauna rikicin siyasa a Burundi inda aka shafe makwanni ana zanga-zangar adawa da matakin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku.

Masu zanga-zangar adawa da Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza da neman wa'adin shugabanci na uku
Masu zanga-zangar adawa da Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza da neman wa'adin shugabanci na uku REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Akalla masu zanga-zanga 20 suka mutu a arangamar da suka yi da jami’an tsaro a tsawon makwanni biyu da aka shafe ana zanga-zanga. Har yanzu kuma ana ci gaba da zanga-zangar a Bujumbura babbar birnin kasar.

Masu zanga-zangar sun ce matakin Nkurunziza na neman wa’adi na uku ya sabawa kundin tsarin mulki da yarjejeniyar Arusha da ta taimaka aka kawo karshen yakin basasa a kasar.

Amma Kotun kundin tsarin mulki tace Nkurunziza na da ‘yancin sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a watan Yuni, domin Majalisa ce ta zabe shi a wa’adinsa na farko.

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane 50,000 suka tsere daga Burundi don fargabar yiyuwar barkewar yakin basasa a kasar.

Shugabannin kasashen Kenya da Rwanda da Tanzania da Uganda da kuma Burundi za su gudanar da taro na musamman a Dar es Salam domin tattauna yadda za a warware rikicin kasar.

An dai shafe shekaru 10 Nkurunziza na shugabanci a Burundi, kuma yanzu yana fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya akan ya yanje kudirinsa na neman wa’adi na uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.