Isa ga babban shafi
Mozambique

Mutane dubu 100 za su rasa muhallinsu a Mozambique

Kasar Mozambique na shirin fara gudanar da sabon tsarin bunkasa harkokin noma a kasar, da nufin fara safarar kayayakin amfani gona zuwa kasashen waje, sai dai wannan tsari zai haifar da barazana ga al’ummar kasar sama da dubu 100 wanda ya zama wajibi su rasa muhallinsu.

Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi
Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi Cristiana Soares
Talla

A cewar Jami’ar kungiyar kare hakkin mazauna yankuna karkara a kasar, Clemente Ntauzazi, wannan sabon tsari da Cibiyar Lurio River valley, za ta kaddamar a kasar, shine irin sa na farko da aka taba gudanarwa acikin wata kasar Afrika, kuma zai samar da cigaba tare da rage rashin ayukanyi a kasar.

Sai dai kuma Clemente ta bayyana furgabata akan yadda wannan sabon shirin da zai samar da hecter dubu 240 na Fillin Noma, zai shafi wasu mutane kasar akalla dubu 500, tare da kuma tursasawa wasu sama da dubu 100 barin muhallinsu.

Clemente ta  ce, yawanci inda za’ayi amfani da su a matsayin gonaki, muhalin kanana monama ne da suka shafe sama da shekaru 30 suna zaune a karkara.

Rahotannin dai na cewa, za’a kashe akalla dala biliyan 4.2 wajen gudanar da shirin, kuma zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar

Kasar Mozambique dai na daya daga cikin kasahen duniya dak e fama da matsanancin talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.