Isa ga babban shafi
Burkina Faso

An soma Tono kabarin Thomas Sankara

A kasar Burkina Faso a yau talata ne za a tono kabarin tsohon shugaban kasar Thomas Sankara wanda aka kashe ranar 15 ga watan oktoban shekarar 1987, A  jiya masu aiki suka tono kabarin biyu daga cikin sojojin da suka rasa rayyukansu tare da shi a yayin wani juyin mulki.

Kabarin Tsohon Shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara
Kabarin Tsohon Shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara RFI/Sébastien Nemeth
Talla

Lauyan iyalan tsohon shugaban kasar Benwende Stanislas Sankara, ya ce bayan tono kabarin wani lokaci a yau, nan take za a balle akwatin da ke dauke da gawarsa domin yin bincike akai, to sai dai wasu daga cikin iyalan Sankara sun ce ba su da tabbaci idan har kabarin da ake shirin tonowa hakika na dan uwansu ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.