Isa ga babban shafi
Najeriya-Nijar

Matsalar lantarki a Najeriya ta shafi Nijar

Matsalar wutar Lantarki da ake fama da ita a Najeriya ta shafi makwabciyarta Jamhuriyyar Nijar inda aka aka shafe kwanaki ana fama da matsalar Lantarkin a Yamai fadar gwamnatin da manyan biranen kasar.

Kasuwar Birnin Yamai a Nijar
Kasuwar Birnin Yamai a Nijar Roland Huziaker
Talla

Matsalar ta samo asali ne daga Najeriya da ke ba kasar Lantarki, kamar yadda Darakta Janar na Kamfanin Nigelec da ke samar da Lantarki a Nijar Alassne Halid ya tabbatar a kafar Telebijin.

An shafe kwanaki babu wuta a Najeriya saboda yajin aikin masu ruwa da tsaki ga harakar samar da Mai, lamarin da kuma ya shafi bangaren makamashi a kasar.

Rahotanni sun ce tun a makon jiya aka shiga matsalar Lantarki a Yamai da Maradi da sauran biranen Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.