Isa ga babban shafi
Faransa-Masar

Le Pen ta yabawa hukumomin Masar

Marine Le Pen Shugabar Jam’iyyar yan ra’ayin rikau a Faransa a wata ziyara da ta kai a kasar Masar ta yabawa gwamnatin wanan kasa kan yadda take murkushe masu tada kayar baya a Masar.Le Pen wadda ke ziyara a birnin Alkahira tace shugaba Abdel Fatah al Sisi ya taka rawar gani wajen abkawa yan tawayen masu tsatsauran ra’ayi wanda hakan babban sako ne ga masu irin wanan akida.

Marine Le Pen Shugabar Jam’iyyar yan ra’ayin rikau a Faransa
Marine Le Pen Shugabar Jam’iyyar yan ra’ayin rikau a Faransa REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Bayan ganawa da Firaminista Ibrahim Mahlab da Babban limamin Masallachin Al Azhar, Yar siyasa Marine Le Pen tace zaben jam’iyyar su a Faransa ya zama wajibi dan goyawa irin wadannan kasashe baya.
Gwamnatin Masar lalle shirye take wajen gani an kawo karshen ta’adanci a wanan kasa,inji wani daga cikin masu Magana da yahu hukumomin na Masar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.