Isa ga babban shafi
Najeriya

Gobarar tankar mai ta kashe mutane 69 a Najeriya

A Najeriya, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu sun kai 69 bayan da wata motar daukar man fetur ta kwace wa direbanta sannan kuma ta fada a cikin wata tashar mota sannan kuma ta kama da wuta nan take.

Wuta a lokacin wata tarzoma
Wuta a lokacin wata tarzoma REUTERS/Yevgeny Volokin
Talla

Lamarin dai ya faru ne a garin Onitsha na jihar Anambra da ke kudancin kasar, kamar yadda Uchenna Ezeh kakakin rundunar ‘yansandan jihar ya tabbatar.

Rahotanni sun ce yanzu haka akwai wasu mutane 7 da ke kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka sama daga wutar da ta tashi a lokacin hatsarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.