Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Buhari na ziyarar aiki a Nijar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara ziyarar aiki a Jamhuriyar Nijar kafin ya tafi Chadi inda ake saran zai tattauna da shugabannin kasashen kan matsalar rikicin Boko Haram da ke barazana ga zaman lafiya a kasashen na yammacin Afrika. Wannan na zuwa ne bayan Shugaban ya kwashe tsawon yinin jiya yana ganawa da manyan hafsoshin sojin kasar game da sanin halin da tsaro ke ciki a Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a Abuja Issoufou facebook
Talla

Shugaban ya isa Nijar a yau Laraba inda ake sa ran zai tattauna da Shugaba Mahamadou Issoufou kan batutuwan da suka shafi tsaro da huldar diflomasiya da ke tsakanin Nijar da Najeriya.

Shehu Garba da ke magana da yawun Buhari ya ce shugaban zai nemi hadin kan Nijar domin yakar Mayakan Boko Haram.

A cewar Garba yadda Boko Haram ke tsallakawa zuwa Nijar idan an kore su daga Najeriya ya zama wajibi ga kasashen biyu su hada kai domin kawo karshen ayyukan kungiyar.

Buhari dai zai shafe kwanaki biyu a Nijar kafin ya mika zuwa Chadi da ke taimakawa Najeriya yakar Boko Haram.

A ranar Juma’a ne aka rantsar da Buhari a matsayin sabon shugaban kasa, kuma ya sha alwashin kawo karshen matsalar mayakan Boko Haram da suka yi sanadin mutuwar mutane sama da 15,000 tare da tursasawa miliyoyan mutane kauracewa gidajensu.

Nijar da Chadi dai na makwabtaka da Jihohin Najeriya biyu Borno da Yobe da ke fama da hare haren Mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.