Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza Zai tattanauwa da ‘Yan adawa

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya ce a shirye yake ya yi tattaunawa da abokan hamayyarsa na siyasa domin warware sabanin da ke tsakaninsu dangane da tsayawarsa takara karo na uku, amma kuma da sharidin cewa ‘yan adawar za su shiga tattaunawar da kyakkyawar manufa.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza AFP/Carl de Souza
Talla

Mai magana da yawun shugaba Nkurunziza Willy Nyamitwe, ya ce shugaban bai kawar da yiyuwar samar da mafita kan rikicin siyasar da kasar ke fama da shi ba, ciki kuwa har da batun tsayawarsa takara a zaben da aka shirya gudanarwar a karshen wannan wata na Yuni.

Batun tsayawa takarar Nkurunziza a wani wa'adi na uku, ba karamin haifar da tashin hankali ya yi a Burundi ba, baya ga rasa rayukan al'ummar kasar.

Suma dai 'yan adawar kasar sunce sun shirya domin komawa teburin tattaunawa domin samawa kasar Maslaha. Masu hasashe dai furgaban cewa rashin dai-daito a Burundi na iya jefa kasar acikin wani hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.