Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

'Yan tawayen Sudan ta kudu sun karbe wuraren hakar man Fetir

A Sudan ta Kudu, Yan tawayen Kasar sun bayyana cewa sun karbe ikon wararen da ake hakar man fetir dake arewacin Kasar bayan shafe tsawon makonni biyu suna gwabza yaki da dakarun gwamnati  

Dakarun Sojan gwamnatin Sudan ta kudu dauke da makamai.
Dakarun Sojan gwamnatin Sudan ta kudu dauke da makamai. REUTERS/James Akena
Talla

Mai Magana da yawun yan tawayen, James Gatdek ya shaidawa kamfanin dillacin labaran faransa na AFP cewa guraban hakar man fetir dake jihar Unity na hannun yan tawayen a yanzu, kuma suna cigaba da kokarin ganin sun sake karbe wani wurin hakar man Fetir din dabam dake jihar Upper Nile.

A cewar mai Magana da yawun yan tawayen, sun dau wannan matakin ne, domin hana gwamanatin Kasar samun kudade daga man Fetir.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.