Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko haram-G7

Najeriya ta nemi taimakon kasashen Turai kan Boko Haram

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jadada matsayin gwamnatin sa na yaki da kungiyar Boko Haram a ganawarsa da Shugabanin kasashen Faransa,Jamus da Canada.Kungiyar da ta jefa al’ummar kasar cikin halin kakanikayi. 

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a lokacin ganawarsa da Angela Merkel a Jamus
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a lokacin ganawarsa da Angela Merkel a Jamus REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Yayin da yake ganawa da shugaban kasar Faransa, Francois Hollande a Jamus, Buhari ya ce Najeriya a shirye ta ke ta karbi duk wani taimako da zai ba ta damar samun nasarar yakin domin samar da tsaro ga al’umar wannan yanki.

Shugaban ya ce gwamnatin sa a shirye ta ke ta hada kai da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya domin murkushe wannan kungiyar da ba ta da nasaba da addinin Islama.

A bangare daya kuma rundunar sojin Najeriyar ta sanar da mayar da cibiyar yaki da Boko Haram zuwa birnin Maiduguri, kamar yadda Daraktan yada labaran rundunar Kanar Sani Usman Kukasheka ya shaida mana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.