Akalla mutane 70 sun mutu a mutsayar wuta tsakanin Sojin Masar da ISIL
Akalla mutane 70 ne suka rasa rayukansu mafi yawa sojoji a wata musayar wuta tsakanin mayakan ISIL da dakarun Kasar Masar a yankin Sinai.
Wallafawa ranar:
A safiyar yau laraba ne mayakan ISIL suka kaddamar da kazamin harin a yankin Sheikh Zuweid dake arewacin kasar kan dakrun sojoji da ‘yan Sanda.
Mayakan dai sun kutsa kai ne acikin yankin dauke da bama-bamai a motoci, a wani yanayi na ba za ta.
Rahotani sun ce wannan harin shine mafi muni da mayakan suka kai a Sinai, tare da amfani da gurneti wajen tarwatsa ofishin ‘yan sandan yankin, baya ga tarwatsa shingayan bincike ababban hawa 15, da kuma harba rokoki a cikin sinai.
Sai dai kuma tuni Sojojin Masar suka far musu ta sama wanda a yanzu haka sunyi nasara kashe 38 daga cikin Mayakan.
Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki biyu, bayan kashe mai shigar da karar kasar Hisham Barakat a wani harin bam a birinin Al-Kahira.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu