Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan ta kudu za ta hukunta Sojojin da ke yi wa Mata Fyade

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta ce, za ta hukunta duk Sojan da aka samu da hannu wajen yi wa Mata fyade, jinjirar kasar da ke fama da yakin Basasa, kamar yadda wani rahoton Majalisar dinkin duniya ya sanar.

Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da ke fada da 'Yan tawayen Riek Machar
Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da ke fada da 'Yan tawayen Riek Machar REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Ma su bincike na tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ta kudu sun bayyana gano aikata kazaman laifukan cin zarafin dan adam da sojojin gwamnatin kasar ta Sudan ta Kudu suka aikata a kasar.

Rahoton ya dogara ne kan bayanan da shaidu 115 da abin ya shafa suka bayar, da kuma shaidun da Majalisar Dinkin Duniya ta tattara daga yankunan da aka aikata wannan mummunan cin zarafin matan da kuma fararen hula a kasar da yaki ya daidaita.

A lokacin da ya ke tsokaci kan rahoton na Majalisar Dinkin Duniya kakakin rundunar Sojan Sudan ta kudu Philip Aguer ya ce, sun karanta rahoton sun kuma ga abin da ya kunsa, don haka sun dau niyar daukar matakan hukunta wadanda aka samu da cin zarafin Mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.