An cafke wanda ya jagoranci hare haren Jos da Zaria
Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun cafke mutumin da ya kitsa munanan hare haren ta’addanci da aka kai a biranen Jos da Zaria wanda ya lakume rayukan mutane sama da 70.
Wallafawa ranar:
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Kanal Sani Usman
Kakakin rundunar Sojin Najeriya Kanal Sani Usman Kukasheka ya ce an cafke mutumin ne da wasu mukararbansa guda biyu a Dadin Kowa daga Gombe lokacin da suke kokarin tserewa.
“Sojojinmu sun yi nasarar damke wadanda suka kai hare hare ta’addanci da aka kai a Masallaci da wurin cin abinci a garin Jos da kuma harin da aka kai a Zaria” a cewar Kanal Sani.
Yanzu haka mutanen suna amsa tambayoyi a hannun Jami’an tsaro.
Kanal Sani ya yi kira tare da neman hadin kan al’ummar Najeriya wajen bayar da goyon baya da bayanai da sirri ga jami’an tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu