Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kai hari a Burutai, kauyen Kwamandan Sojin Najeriya

Rahotanni daga Jihar Borno na cewa Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari a garin Buratai, cibiyar sabon babban hafsan Sojin Najeriya, inda mayakan suka kona gidaje ciki har da na ‘yan uwan  kwamandan Sojin kasar  da ya sha alwashin murkushe mayakan da ke addabar arewacin Najeriya.

Janar Tukur Yusuf Buratai Nigerian Babban kwamandan Sojin Najeriya
Janar Tukur Yusuf Buratai Nigerian Babban kwamandan Sojin Najeriya nigerian defence
Talla

Akalla mutane biyu suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, kamar yadda wasu Mazauna garin na Buratai suka tabbatarwa Kamfanin dillacin labaran Reuters.

Majiyoyin sun ce an kai harin ne a ranar Talata, amma ko da aka kai harin Babban Hafsan Sojin kasar Janar Tukur Buratai baya cikin garin.

Janar Tukur Buratai dai shi ne sabon babban hafsan sojin Najeriya da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada, wanda ya sha alwashin murkushe ayyukan mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.