Isa ga babban shafi
Boko Haram

Buhari ya kammala ziyara a Kamaru

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kammala ziyarar aiki a kasar Kamaru inda ya tattauna da takwaransa Paul Biya kan matsalar ayyukan Boko Haram da ke addabar kasashen biyu.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kai ziyara Kamaru bayan ya je Nijar da Chadi kan matsalar Boko Haram
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kai ziyara Kamaru bayan ya je Nijar da Chadi kan matsalar Boko Haram AFP PHOTO / CAMEROON PRESIDENCY
Talla

A lokacin da ya ke jawabi bayan ya gana da shugaban Kamaru, Buhari ya ce ya zama wajibi a gare su da su tunkari babban makiyinsu, Boko Haram domin matsala ce da ta haifar da hasarar rayuka sannan ta jefa dimbin jama’a a cikin kuncin rayuwa a kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi.

Buhari ya ce Najeriya a shirye ta ke ta kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram da ta yi sanadiyar hasarar rayukan dubban mutane da kuma dukiyoyinsu.

Sannan Shugaban na Najeriya ya ce kasa guda ba zata iya maganin Boko Haram ba dole sai an hada kai, don haka suka kafa runduna ta musamman da zata kawo karshen ‘Yan ta’adda.

A nashi bangaren, shugaban Kamaru Paul Biya, wanda ke gabatar da jawabi a gaban shugaban na Najeirya, ya ce zuwan Buhari a Kamaru wata alama ce da ke tabatar da cewar shugaban na a cikin shiri domin kawo karshen matslar Boko Haram.

Biya, ya ce ya yi imani shugaba Buhari na fatar ganin an kawo karshen matsalar Boko Haram, kuma yana son hada kai da sauran kasashen da abin ya shafa domin samun nasara, domin ziyarar da ya kawo a Kamaru da kuma tattaunawar da suka yi ta kara tabbatar da da gaske ya ke.

A Ziyarar dai Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan Najeriya mazauna kasar Kamaru inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi Najeriya da kuma zamantakewarsu a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.