Najeriya
Majalisar Dattijai ta dage ranar tantance shugabannin tsaron Najeriya
Majalisar dattawan Najeriya ta dage ranar da za ta soma aikin tantance sabbin shugabannin rundunonin tsaron kasar da shugaban Muhammadu Buhari ya nada, aikin da ya kamata majalisar ta fara a yau Alhamis amma sai zuwa ranar talata ta makon gobe.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugaban Majalisar dattawan Bukola Saraki, da farko ya ce za su fara aikin tantancewar ne a yau, kafin daga bisani ya ce sai a ranar Talata mai zuwa.
Majiyoyi sun ce an dage zaman ne domin samun damar halartar bukuwan karrama tsohon babban kwamandan askarawan kasar Alex Badeh da za a yi a yau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu